Matafiya masu fita kasashen waje a Najeriya na iya nema tare da samun ‘ingantattun katunan shaidar rigakafin COVID-19 a cikin ƙasa da sa'a ɗaya kafin keta hazo ba tare da an yiwa mutum rigakafin ba. Almundahanar bayar da shaidar rigakafin Corona na cigaba da karuwa a Najeriya.
Wannan ne jigon rahotonmu na musamman a wannan mako, da wakilinmu Kolawole Omoniyi ya hada mana, inda masana ke cewa al’amarin ba kawai bata sunan Kasa ke yi ba harma da zama barazana ga harkokin lafiya.
Alemeke Bright, jagora ne na ‘yan cuwa-cuwa a cibiyar lafiya dake filin tashi da saukar jirgin saman kasa-da-kasa na Murtala Muhammed, dake Legas.
Bright ya 15,000 a hannu wakilinmu, inda ya samar masa da katin COVID cikin kasa da mintuna 30, ga yadda abin ya faru.
Abin mamaki shine da aka sanya lambar QR code, bayanansa sun bayyana a runbun ajiya na Hukumar kula da Lafiya a matakin farko ta kasa NPHCDA.
Matafiya irinsu Agboiyi Peter, na daga cikin irin Mutanen da Bright ke burin samu. Shima Peter ya sami katin COVID ta hannun Bright, don guje wa damuwa daga jami'an filin jirgin.
Yawancin lokaci Bright, na jiran masu bukatar katin a ƙofar shiga cibiyar lafiyar PHS, ya gamsar da su da cewa ba sai sunyi rigakafin ba.
Da aka tuntube, Shugaban cibiyar lafiyar matakin farko dake filin jirgin na Legas, Dokta Omide Ogu, yace bai san Bright ba.
Ya kara da cewa yanzu Mutane sun rage yin rigakafin COVID a cibiyar sakamakon sassauta yin allurar ta COVID da gwamnatin Kasar nan ta yi.
Dr. Ogu bai san cewa ana sabi zarce da masu bukatar allurar a cibiyar tasa zuwa cibiyar lafiya a matakin farko na Mafoluku dake da kimanin kilomita 10, inda Mr. Bright da Mutanen sa, ke bada kati ba tare da yin allurar ba.
Ana hada-hadar katin COVID sosai a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers.
Duk da cewa an dakatar da dokar tilasta allurar rigakafin a filin jirgin sama na kasa da kasa da ke can, amma yawancin kamfanonin mai na kasa da kasa na sanya dokar nuna katin kamar yadda wata mai yin allurar rigakafin, Esther ta yi bayani.
Esther bata yin alluran rigakafin sai dai ta karbi na goro ta bada katin. ta danganta matakin na ta da gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan ta alawus-alawus dinta.
Zainab Umar, dake cibiyar lafiya ta Gwagwalada a birnin tarayya Abuja, itama tace ba a biyansu alawus-alawus din su.
Ta nemi wakilinmu ya biya 10,000 ta bashi katin nan take.
Hakan take a cibiyoyin lafiya na nan Kano. A asibitin Koroda, wani jami'i, Ahmed Sani ya dage sai an biya 10,000, ya samar da katin ba tare da yin allurar ba.
Mahajjata da dama da ke zuwa Saudiyya na karbar katin ba tare da yin allurar rigakafi ba.
Ko da aka tuntubi jami’in rigakafi na nan Kano, Dakta Shehu Abdullahi Mohammed, ya danganta rashin gaskiyar da cuwa-cuwa da samu da gazawa wajen tursasa bin doka.
Ya bayyana yadda wasu daga cikin Jami'an riga kafi ke zubar da ruwa maganin da ba a yi amfani da su ba.
An dorawa hukumar kula da lafiya a matakin farko ta kasa alhakin kula da allurar rigakafi a duk fadin Kasar nan. Dukkanin Kokarin jin ta bakin Babban Daraktan ta, Dakta Faisal Shuaib, tsawon watanni uku ya ci tura.
Da aka tuntubi, wata kwararriyar likita a Asibitin Koyarwa na Legas, Dokta Alero Roberts, ta ce duk da cewa cutar ta COVID-19 ta lafa, har yanzu yin allurar riga-kafi nada matukar muhimmanci.
Ta nuna damuwata kan yadda ake samun katin ta bayan fage, tana mai cewa yin hakan na iya kowa cikas wajen dakile wannan annobar dama wadda ka iya tasowa a nan gaba.