On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Ya Zama Tilas Masu Son Shiga Jami'a Kai Tsaye Su Rubuta Jarabawar UTME

JAMB

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta kasa JAMB, ta ce daga yanzu ya zama wajibi masu neman shiga jami’a kai tsaye su rika rubuta jarabawar UTME , tare da sauran wadanda suke zama domin rubuta jarabawar.

Hukumar  ta ce sabon matakin wani yunkuri  ne na  tabbatar da cewar  masu son  shiga jami’ar kai tsaye, sun tabbatar da abunda suka  karanta  a  matakin  farko.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban sashin hulda da jama’a na hukumar, Fabian Benjamin ya fitar  a Abuja, jim kadan bayan kammala wani taron kolin  hukumar.

Y ace  an  shirya  taron ne domin yin duba kan yadda  aka  gudanar da rijistar masu son shiga  jami’a kai tsaye a kwanan nan.

Ya kuma  ce  matakin zai magance  matsalolin da ake  samu  kan batun samun gurbin shiga jami’a kai tsaye.