Shugaban jam’iyyar APC na kasa,Sanata Abdullahi Adamu ya bukaci shugaban kasa Muhammad Buhari da ya mutunta umarnin da kotun koli ta bayar kan batun canjin kudi.
Da yake yiwa manema Labarai a sakatariyar jam’iyyar dake Abuja, Shugaban jam’iyyar, Ya ce wasu manyan jami’an gwamnatin kasar nan guda ukku sun mutunta umarnin da kotun kolin ta bayar, domin rage radadin da jama’ar kasa suke a ciki.
Bugu da kari ya ce rashin martaba umarnin da kotun kolin ta bayar, wata babbar tawaya ce ga cigaban fannin tattalin arzikin kasa.
Idan ba’a manta ba, Kotun kolin ta umarci babban bankin kasa da kasa ya fara aiwatar da tsarin na dena amfani da tsohon kudi a ranar 10 ga watan da muke ciki, har sai zuwa lokacin da kotun zata kammala sauraren shari’ar da aka shigar gaban ta, To sai dai Shugaban kasa Buhari da kuma babban bankin kasar sun bijirewa wannan umarni.