Hukumar Lafiya ta duniya, tayi kira da a dauki matakan gaggawa domin dakile bazuwar cutar Kyandar Biri a nahiyar Turai, Inda ta baiyana cewa an samu rubunyar masu harbuwa da cutar a cikin makwanni biyu da suka gabata.
Tun a farkon watan Mayun Bana ne, aka samu fantsamar cutar Kyandar Biri a kasashe yammacin Afrika da kuma na tsakiya , inda aka fi samu bazuwar ta.
Kaso 99 bisa 100 na gwaje-gwajen da aka yi sun tabbatar da cewa , mutane Dubu 4 da 500 da suka kamu da cutar sun fito ne daga nahiyar turai.
Bugu da kari a yanzu haka kasashe 31 aka samu rahoton cewa sun kamu da cutar.