Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi na biyu, ya shawarci gwamnati mai jiran gado da ta dauki darasi daga kura-kuran gwamnatocin da suka shude suka yi, ta hanyar nada kwararrun mutane a mukamai da za su bunkasa cigaban kasa.
Da yake jawabi a yayin taron kaddamar da wani littafi a Abuja ranar Talata, Malam Muhammadu Sanusi ya ce yana fatan ganin jerin sunayen ministocin da shugaban kasa mai jiran gado zai nada.
Ya kuma yi kira ga gwamnati mai zuwa da ta kare hukumomin gwamnatin kasar daga abunda ya baiyana na ‘Yan Siyasa masu wuce gona da iri.