On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Wike Ya Musanta Sayen Mota Mai Sulke Ta Milyan 300 A Lokacin Da Ya Hau Matsayin Ministan Abuja

Wike

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya musanta rahotannin dake cewar ya sayi wata sabuwar mota mai sulke kirar Lexus akan tsabar kudi naira milyan 300, daga hawansa matsayin ministan Abuja.

Ministan ya  karyata rahotannin ne jim kadan bayan wata ziyarar gani da ido da ya kai,  tashar  jirgin kasa  ta Abuja,domin duba yadda ake  gyara sufurin  jirgin kasan Abuja ke  kasancewa.

An dai nuna hoton wata  sabuwar  mota kirar Lexus  mai sulke,mai dauke da  lambar FCT 01, Da aka baiyana cewar  tsohon  gwamnan jihar  Ribas din ne ya saye  ta.

Rahotanni sun baiyana cewar sabuwar  motar  wadda kudinta ya kai naira milyan 300  ta kasance  mallakin ministan Abuja,Nyesom Wike.