On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Wike Ya Ce Sai Da Ya Samu Izinin Shugabannin PDP Kafin Ya Karbi Matsayin Minista

WIKE

Sabon ministan birnin taraiyya Abuja, Nyesom Wike, Ya ce sai da ya samu izinin jagororin jam’iyyar PDP,kafin ya amince da tayin zama minista a gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu.

Kafin nada shi  kan matsayin minister da shugaban kasa  ya yi,  Wasu daga cikin  ‘yan jam’iyyar PDP sun rika kokarin ganin an dakatar da shi daga jam’iyyar,sakamakon alakar  da yake  da  ita  tsakaninsa  da  ‘yan jam’iyyar  APC, da kuma amincewa  da karbar matsayin ministan  da  ya yi.

Sai dai a yayin taron manema Labarai  da  minista Wike ya yi a jiya, jim kadan bayan rantsuwar  kama aiki,  Ya  tabbatar da cewar sai da ya rubuta wasika  ga shugabannin jam’iyyarsa, cikinsu hadda mukaddashin shugaban jam’iyyar  PDP na kasa, Iliya Damagum , Kuma ya samu amincewarsu  na zama minista a gwamnatin Tinubu.

Sabon ministan Abujar ya yi barazanar rushe  duk  wasu  gine-gine da aka yi wanda suka ci karo da taswirar  birnin  taraiyya Abuja.