Jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB Mazi Nnamdi kanu Ya sake yin nasara a karar da ya kai gwamnatin tarayya a yayin da wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Umuahia, ta goyi bayan Hukuncin da wata kotu tayi masa na bashi nasara akan shari'ar dake tsakaninsa da gwamnatin tarayya.
Kotun karkashin jagorancin, mai shari’a Everlyn Anyadike ta bukaci Gwamnatin tarayya da ta biya shi Naira milyan 500.
Wannan dai shine hukunci na biyu da wata kotu ke yi, kuma Nnamdi Kanu ke samun nasara akan gwamnatin taraiyya.
Koda a yan makwannin nan wata Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta bada umarnin a saki Nnamdi Kanu, Sai dai kuma gwamnatin taraiyya, ta hannun babban lauyanta Abubakar Malami SAN, Yace hukuncin kotun ya ta'allaka ne kawai kan yadda aka dawo da jagoran kungiyar IPOB gida Najeriya, Amma bai shafi sauran tuhumar da ake masa ba, ta aikata lefin ta'adanci da cin amanar kasa.