On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Wata Mata Ta Haihu A Filin Kwallo Ana Tsaka Da Rabon Tallafi A Kano

Wata mata 'yar shekaru 30 mai suna Hadiza Ayuba, ta haifi ‘ya mace a filin kwallo na Dr. Abdullahi Umar Ganduje dake karamar Hukumar Dawakin Kudu lokacin da ake taron raba tallafi wa mata masu juna biyu ranar Asabar.

Taron raba kayan tallafin shi ne karo na hudu da mamba mai wakiltar kananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa, Hon. Mustapha Bala Dawaki yake shiryawa. “A wannan karo, an shirya tallafawa mata 900 daga mazabu 30 na kananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa," in ji Babannan Bala, ma’ajin jam’Iyar APC na mazabar Dawaki.

'Dan jarida Musbahu L Hamza ya rawaitowa Arewa Radio cewa, ana tsaka da taron, bayan Mallaman lafiya daga babban Asibitin Mallam Aminu Kano (AKTH) sun kammala bitar wa mata masu juna biyu, Hadiza Ayuba ta fara nakuda, inda ba a yi wata wata ba aka garzaya da ita bayan kangon filin taron domin bata kulawa na musamman. An kuma bata nata tallafin kai tsaye.

Tallafin ya kunshi bahun din wanka, da sauran abin da mai haihuwa ke bukata.

Hadiza ta sanar da  Misbahu el-Hamza cewa za ta sawa 'yar tata suna Hajara nan da kwanaki bakwai.