Wata mata mai tsohon ciki da yan bindiga suka sace a cikin watan Yulin Bana a Mando dake jihar Kaduna, ta haifi santalelen jariri a wurin da ‘yan bindigar suke tsare da ita.
Rahotanni sun baiyana cewa matar ta fada komar yan bindigar ne akan hanyarta ta zuwa duba mahaifiyarta dake fama da rashin lafiya , inda aka sace ta tare wasu yan uwanta mata biyu.
Da yake tsokaci kan al’amarin, Mijin matar mai suna Mohammed Alabi, Yace mai dakin nasa ta haihu a hannun masu garkuwar a ranar Biyu ga watan Augustan bana, kuma babu wata kulawa da mai jegon tare da jaririn suka samu.
Alabi ya koka kan yadda yadda masu garkuwar ke azabtar da iyalin nasa, inda yace da farko sun nemi a basu naira milyan 140 kafin daga bisani su mayar da ita zuwa naira Milyan 50.