Gamayyar kungiyoyin farar hula na Arewa sunyi gargadi kan yunkurin da gwamnatin jihar Kano ke shiryawa na yiwa tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ‘keta.
Kungiyar ta ce akwai wata makarkashiya da gwamnatin jihar ta shirya na bata sunan Ganduje ta hanyarsiyasa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.
A cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar Muhammed Lawan Shuaibu ya fitar, kungiyar ta nunar da cewa ana yunkurin ne domin bata sunan tsohon gwamnan da ke da kyakkyawar alaka da shugaban kasa Bola Ahamed Tinubu.
Kungiyar da ke karkashin kungiyar kungiyar rajin tabbatar da shugabanci Nagari ta kuma yi ikirarin cewa gwamnatin Kano ta dauki matakin ne domin hana Ganduje samun mukaman siyasa a matakin tarayya.