Wata kungiya mai suna National Rescue Movement ta yi karar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi a gaban kotu bisa zargin mallakar shaidar dan kasa biyu.
A wata kara aka shigar a babbar kotun tarayya, kungiyar ta zargi Peter Obi da samun shaidar zama dan kasa a birnin Dallas dake jihar Texas ta kasar Amurka wanda ya sabawa sashe na 1 da 137 na kundin tsarin mulkin Najeriya.
Masu shigar da karar na neman kotu ta bada umarnin dakatar da Obi daga takarar shugaban kasa sannan a bada umarni na har abada da zai hana INEC baiwa Obi wani hakki ko wata dama ta tsayawa takarar shugaban kasa.
Sai dai mai shari’a Inyang EdemEkwo ya soki masu shigar da karar bisa gaza gabatar da sammacin wadanda ake kara sannan ya sanya ranar 10 ga watan Fabrairu domin fara shari’ar.