Wani rikici ya kunno kai a fannin ilimi a Kano yayin da gamayyar kungiyoyin masu makarantu masu zaman kansu ke barazanar daukar matakin shari’a akan Comrade Baba Abubakar Umar, mai baiwa gwamna shawara na musamman kan zargin abun suka bayyana amatsayin ikirarin karya da wasu kalamai na cin zarafi da tsarotarwa da yake yi akansu.
Ƙungiyoyin sun bukaci mai bada shawara na musamman ga gwamnan kan makarantu masu zaman kansu da ya fito fiti ya nemi Afuwarsu a bainar jama’a ba tare da wani sharadi ba, wanda rashin yin hakan ka iya tunzura kungiyar ga daukar matakin shari’a
Da yake jawabi a madadin gamayyar da yammacin jiya Laraba, daya daga cikin masu ruwa da tsaki a kungiyoyin, Injiniya Bashir Adamu Aliyu, ya ce Baba Umar ya zargesu da laifin yin jabun takardar rajista, rashin fitar da haraji ga gwamnati da karin kudin makaranta ba bisa ka’ida bad a raina gwamnati da dokokinta da kuma Tsauwalawa Iyayen yara da dai sauransu.
Aliyu, yayin da yake musanta dukkannin ikirarin, ya bukaci Gwamna Abba Kabir ya sanya baki domin masu Makarantu masu zaman kansu na cikin masu ruwa da tsaki a jihar Kano dake tallafawa Ilimi.
Da yake mayar da martani, Baba Abubakar Umar ya bukaci kungiyoyin da su aiwatar da barazanarsu, inda ya jaddada cewa dole ne masu makarantun su bi dokar makarantu masu zaman kansu ta 2014.