Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, ta ce, ta gano kullin da wasu ‘yan siyasa ke yi na kera na’urar tantance masu zabe ta zamani BVAS, domin yin magudi a zaben shekara mai zuwa.
Shugaban sashin wayar da kan masu zabe na hukumar, Achumie Rex ne ya baiyana haka a ranar Laraba, a yayin da yake jawabi a wajen wani taron karawa juna sani na yini biyu da aka shiryawa kungiyoyin farar hula, akan kada kuri’a.
Ya kara da cewa wasu daga cikin yan siyasar na kokarin yin kutse a babban rumbun ajiyar bayanan hukumar dake kan internet gabanin babban zaben kasar nan dake tafe, ya kuma kara da cewa hukumar ta dauki dukkanin matakan da suka dace, domin dakile yunkurin ‘yan siyasar.
Daga nan sai ya sake jaddada yunkurin hukumar zabe ta kasa INEC, na gudanar da sahihin zabe a shekara mai zuwa.