Gabanin rantsar da zauren majalisar dokokin kasa na goma a yau, Wasu ‘yan jam’iyyar APC da suka taso daga jihar Imo,domin halartar bukin rantsuwar sun gamu da ajalinsu, sakamakon hadari da suka yi.
Kakakin jam’iyyar APC a jihar Imo, Cajetan Duke ya tabbatar da faruwar abun alhinin, inda ya baiyana cewar motar da mutanen ke ciki ta yi karo da wata motar Bas a jihar Delta.
Ya tabbatar da mutuwar mutane biyu a yayin da wasu suka ji raunika , inda aka garzaya dasu Asibiti domin samun kulawar gaggawa.
Mai magana da yawun jam’iyyar ta Apc Ya lamarin a matsayin mai sosa zuciya.