On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Wasu Tsaffin Gwamnonin PDP Tare Minista Wike Sun Gana Da Shugaban Kasa

WIKE DA SHUGABAN KASA

Ministan Abuja Nyesom Wike ya jagoranci tawagar tsaffin gwamnonin guda hudu da kuma guda daya dake kan mulki a halin yanzu, inda suka gana da shugaban kasa Bola Tinubu a daren jiya.

Rahotanni sun baiyana cewar  an  fara yin  ganawar ne a gidan minista Wike dake Abuja, kafin daga bisani su garzaya wajen shugaban kasa Bola Tinubu a fadarsa dake Villa Abuja.

Duk da cewar  babu bayanin abunda  ganawar ta kunsa, sai dai wasu rahotanni na baiyana cewar ganawar  tasu bata rasa nasaba da inganta alaka tsakanin tsaffin gwamnonin da kuma  shugaban kasa.