On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Wasu Mata Da Iyayen Marayu A Jihar Kano Na Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa

Tabarbarewar tattalin arziki da ya biyo bayan cire tallafin man fetur a Najeriyqa, ya tilastawa mata da Iyayen marayu a Kano gudanar da zanga-zangar lumana, inda suke bukatar  hukumomi su dauki matakin magance matsalolin tsadar rayuwa.

Idan dai za a iya tunawa gwamnatin jihar Kano ta ce ta Siyo kayan abinci da ya kai naira biliyan 1 da dubu dari 6 domin rabawa talakawa kyauta, sai dai ba a fayyace ranafara rabon tallafin ba da kuma yadda za a raba.

Matan da suka fito daga Ja’een da makwaftan unguwanni dake  kananan hukumomin Gwale da Kumbotso, ana tsaka da ruwan sama da yammacin ranar lahadi sun sha alwashin yin tattaki har zuwa gwamnatin Kano domin isar da kokensu.

Sun yanke shawarar cewa tallafin ba dole ba ne ya kasance kyauta, maimakon hakan a rage farashin abincin domin mutane masu yawa su samu damar amfana.

Shugabannin masu zanga-zangar, Habiba Sulaiman Umar da Maryam Abdullahi Muhammad, sun ce yanayin tattalin arzikin ya gurgunta kananan sana’o’insu na cikin gida.