
Sama da jiga-jigan siyasa 40, wadanda suka koma jam’iyyar NNPP, tare da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shakarau, sun yanke shawarar ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar.
Sun kuma jaddada biyayyar su ga jam’iyyar tare da yin alkawarin yin aiki domin ganin ta samu nasara a babban zaben 2023.
Manyan jiga-jigan jam’iyyar ta NNPP sun bayyana matsayarsu ne a cikin wata sanarwar da suka fitar a karshen wani taro da suka gudanar, wanda dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Karaye da Rogo, Haruna Isa-Dederi, ya karanta matsaya amadadinsu.
Rahotanni sunce, dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da mataimakinsa, Aminu Abdulsalam da dan takarar Sanatan Kano ta Kudu Abdurahman Kawu-Sumaila, na daga cikin wadanda suka halarci taron.