Gwamnonin jam’iyyar PDP biyar da ke adawa da halin da ake ciki a jam’iyyar a ranar Lahadi sun yi wata ganawa a fadar gwamnatin jihar Enugu kan wani sabon salo ko dabaru ga jam’iyyar.
Tawagar da Gwamna Nyesom Wike ya jagoranta sun hada da Seyi Makinde na Oyo, Okezie Ikpeazu na Abia sai Samuel Ortom na Benue, das hi kansa Nyesom Wike na Rivers da kuma mai masaukin baki Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu sun hadu kusan mako guda bayan da dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar ya ziyarci jihar.
Gwamnonin sun yi ganawar sirri tsahon sa’o’i kadan kuma sun ki yin magana da manema labarai a karshen ganawar.
Jam’iyyar PDP dai ta fada cikin rikici ne tun bayan zaben fidda gwani na shugaban kasa a watan Mayu, yayin da gwamnonin suka dage sai shugaban jam’iyyar na kasa Iyorcha Ayu ya sauka daga mukaminsa, tun bayan ayyana tsohon mataimakin shugaban kasa Abubakar amatsayin dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.