Wani abun alhini ya faru a gefen gabar tekun Elegushi da ke unguwar Lekki a jihar Legas, bayan da wasu matsakaitan matasa hudu suka nutse cikin ruwa a lokacin da suke tsakaya da yin ninkaya a wajen.
Matasan wadanda basu jima da kammala kwalejin Kuramo dake yankin na Lekki ba, sun je yin iyo ne a bakin ruwan domin murnar kammala rubuta jarrabawar WAEC lokacin da lamarin ya faru.
Mai magana da yawun hukumar kula da gabar tekun Elegushi, Cif Ayuba Elegushi, a ya ce Daliban basu bi ka’idar data dace wajen yin ninkayar ba.
Ya kara da cewa abun ya faru ne a wani waje da ba’a barin mutane suje domin yin wanka a gabar tekun.
A wani bangaren kuma, wani Mai Babur mai kafa biyu ya rasa ransa sakamakon wata arangama tsakanin Yan Acaba da ‘yan sanda kan wani hatsarin da ya faru a unguwar Abule-Egba da ke jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata ta cikin wani sako daya wallafa a shafinsa na Twitter.
Sai dai kuma yace an samu lafawar kura bayan da aka tura jami'an yansanda wajen da abun ya faru.