Tsohon Karamin Ministan Ilimi na kasar nan, Chukwuemeka Nwajiuba da kuam wata kungiyar amintattu mai rajin kare hakkin al’umma ta duniya, Sun shigar da wata kara gaban wata babbar Kotun taraiyya dake zamanta a Abuja, Inda suke neman a aiyana Tsohon Ministan Ilimin a matsayin halastaccen Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC.
Kazalika masu karar sun bukaci kotun ta soke takarar Bola Tinubu na jam’iyyar APC da kuma ta Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP.
Tsohon Karamin ministan Ilimin wanda ya sayi fom din yin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC a kan tsabar kudi har naira milyan 100 ya tashi da kuri’a daya ne kacal a zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam’iyyar APC da aka yi ranar 8 ga watan jiya, inda ya zargi Tinubu da Atiku da siyan wakilan jam’iyyarsu da Kudaden Dollar.
Mister Nwajibu ya bukaci kotun ta soke takarar Atiku da Tinubu a sakamakon cin hancin da suka bawa wakiln jam’iyya domin ganin sun samu nasara.
Masu shigar da karar sun hada kunshin kararssu da wani faifan bidiyo a matsayin shaida wanda ke nuna tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, yana kokawa kan yadda Deligate din jam’iyyar APC suka siyar da kuri’unsu a yayin zaben fidda gwani na shugaban kasa.