Rundunar Yansandan jihar Kano ta tabbatar da kisan gillar da aka yiwa wani mai suna Abdulrrahma Usman a Panshekara Wanda Wani Dan Adaidaita sahu da ba’a kaiga tantacewa ba Ya aikata
Wakilinmu Bashir Faruk Durumin Iya, Wanda ya ziyarci yankin ya ruwaito mana cewa, Mai Babur din Adaidaita Sahun ya dabawa Marigayin Almakashi ne da karfe 9 na dare kafin daga bisani ya cika wandonsa da Iska.
Wani ganau wanda ya kasance abokin Marigayin mai suna Aliyu Muhammad, Yayi karin haske kan yadda aka halaka abokin nasa, wanda aka bari cikin jini male-male bayan sa’in sar data kaure a tsakaninsu.
Kazalika shima kakakin Rundunar yansandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarnin.