Wani Lauya Mazaunin jihar Enugu, Ogochukwu Onyema ya garzaya babbar kotun tarayya dake zamanta a jihar, inda ya Roki kotun data ayyana kujerar mazabar Enugu ta yamma amatsayin babu kowa tare da sanya sunansa amatsayin wanda zai maye gurbin sanatan.
Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, sanata Ike Ekweremadu shine sanata dake wakiltar wannan mazaba ayanzu haka wadda kuma ta kasance mahaifar Lauyan
Onyema ya Bukaci kotun data ayyana kujerar amatsayin babau kowa, asakamakon cigaba da tsare Dana majalisar a kasar Burtaniya, inda ake tuhumarsa da alaifukan da suka Danganci safarrar sassan jikin Dan ‘adam , Acewar Onyeama bai kamata acigaba da barin kujerar babu kowa ba ayyainda Ekweremadu ke tsare
A shari’ar da aka shigar a babbar kotun tarayya, Enugu, Onyema ya kuma roki kotun data bada umarni da kuma baiwa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu da jam’iyyar PDP su zabi, tare da mika sunansa ga Majalisar Dokoki ta kasa a matsayin wanda zai maye gurbin Ekweremadu.
Hakazalika ya kuma roki kotun data umarci Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa Farfesa Mahmood Yakubu da Hukumar ta INEC su janye ko soke takardar shaidar cin zabe a baya da aka baiwa wanda ake kara na 3 (Ekweremadu) tare mika masa Shaidar cin zaben