An tabbatar da mutuwar wasu kananan yara takwas tare da wani mai gadi bayan wani yaro dan shekara 14 ya bude wuta a wata makaranta da ke Belgrade, babban birnin kasar Sabiya. Kazalika an samu wasu kananan yara da ma’aikata da dama sun samu raunuka.
Kakakin ‘yan sandan birnin Belgrade, Veselin Milic, ya ce wanda ake zargi da aikata ta’adin ya kira hukumomi domin su kama shi a harabar makarantar.
Milic ya ce maharin ya shirya kai harin wata guda da ya gabata, kuma an gano cewar bindigar da yaron ya yi amfani da ita ya dauko ta ne daga inda mahaifinsa yake ajiye bindigar.
Ministan ilimi na kasar Serbia Branko Ruzic, ya bayyana kaduwarsa kan faruwar harin ta’addancin, inda ya alakanta faruwar lamarin da tasirin kafofin sadarwa ke dashi da kuma wasanni tare da kallon fina-finai na kasashen turai da ake yi.
A yanzu haka an ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki uku a fadin kasar ta Sabiya.