Wani jirgin dakon kaya ya yi hadari a kusa da birnin Kavala da ke arewacin kasar Girka.
Jirgin mai suna Antonov-12 mallakin wani kamfani da ke Ukraine ya taso ne daga Sabiya zuwa Jordan a lokacin da ya rikito a jiya. Kawo yanzu Ba a kaiga sanin adadin mutanen da ke cikin jirgin, ko kuma sanin wadanda suka tsira.
Rahotanni sun baiyana cewa matukin jirgin ya yi kokarin yin saukar gaggawa a filin jirgin Kavala saboda matsalar da injin jirgin ya samu amma jirgin ya kasa isa titin jirgin.
Mahukuntan yankin sun ce an tura motocin kashe gobara bakwai amma ba su iya tunkarar wurin da hadarin ya faru ba, saboda yadda jirgin ke cigaba da tarwatsewa a lokacin.