On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Wani Dattijo Da 'Dansa Sun Gamu Da Ajalinsu Sanadiyar Yasar Rijiya A Kano

Wani mahaifi mai shekara 60 a duniya, Malam Bala da dansa mai shekara 35, Sunusi Bala sun gamu da ajalinsu a cikin wata rijiya da ke Sabon Garin Bauchi, a karamar hukumar Wudil ta jihar Kano a ranar Talata.

Wata sanarwa da kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi ya fitar ta ce an kira mahaifin da dansa domin su yi yasar rijiya kafin faruwar al’amarin.
A cewarsa, sun yi nasarar yashe rijiyar kafin dan ya makale a lokacin da ya koma karasa gyara yasar rijiyar.
Abdullahi ya kara da cewa mahaifin Sunusi shi ma ya makale ne a lokacin da yake kokarin ceto dansa saboda rashin iskar a cikin rijiyar. 
Ya ce an mika gawarwakinsu ga  ofishin ‘yan sanda na model dake garin Wudil.