Wani Bene mai hawa bakwai da ake kan aikin gina shi a yankin Banana Island dake birnin Ikko ya ruguje, wanda hakan yayi sanadin makalewar ma’aikata da dama a cikin baraguzan ginin.
Jami’in Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa reshen jihar Legas shine ya tabbatar da faruwar abun alhinin a ranar Laraba,lokacin da yake ganawa da manema Labarai.
Bugu da kari shima kakakin Ma’aikatar Kasa da tsare-tsarenta ta jihar Legas, Munkaila Sanusi ya tabbatar da cewar ba’a samu asarar rai ba, inda banda wadanda suka samu raunika da ake kan dubasu yanzu haka.
Ya kara da cewar Benen da ake kan aikin ginawa bai samu amincewa daga hukumomin da suka kamata ba.