Wani basaraken gargajiya na yankin Aghara dake karamar Hukumar Kabba Bunu a jihar Kogi mai suna Chief David Obadofin da aka yi garkuwa dashi, Ya mutu a hannun masu garkuwar.
Rahotanni sun baiyana cewar basaraken ya mutu ne a ranar Alhamis din data gabata bayan shafe kwanaki 12 yana a hannunsu,Inda ta kaiga ko tsayawa baya iya yi,sakamakon U’kubar da masu garkuwar suka gana masa.
Basaraken wanda ya kasance babban manomin Yazawa a yankin, Anyi awon gaba dashi ne a lokacin da ake bukukuwan Easter da karfe 11 na dare lokacin da yake cikin wani gidan gonarsa.
Rahotanni sun baiyana cewar yan bindigar sun amince su karbi naira milyan 2 lokacin da suka fahimci basaraken na halin gargara, kafin su sakeshi tare da wata mai suna Temidayo.
Daga karshe macen ta kubuta a hannunsu a yayin das hi kuma rai yayi halinsa kafin a kaiga biyan kudin fansar, Kazalika Masu garkuwar sun bindige wata bazawara mai suna Toyin Onare wadda ta kasance ma’aikaciya a gidan gonar.