Wasu rahotonni da ba a tabbatar ba na nuni da cewa akwai yiwuwar tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje zai maye gurbin Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.
Bayanan sunce shugaba Bola Tinubu yana nazarin neman a baiwa Ganduje shugabancin APC domin maye gurbin Adamu.
Rahotanni a daren jiya na cewa an cire sunan Ganduaje daga jerin sunayen ministocin Tinubu kuma majiyoyi sun nuna cewa Tinubu ya gamsu sosai da zabin Ganduje.
Zamu kawo muku karin bayani akan batun.