Jam'iyyar APC ta rufe gabatar da shaidu a gaban Kotun sauraran karar zaben gwamnan Kano da shaidu 32
Yayin zaman Kotun Jam'iyyar APC ta gabatar da Engr Rabi'u Sulaiman Bichi da Dr Aminu Idiris Harbau daga Kwalejin Sa'adatu a matsayin shaidun Kwarewa
Engr Rabi'u Sulaiman Bichi ya shaidawa Kotu cewa dantakarar Jam'iyyar APC Dr Nasiru Yusuf Gawanu be taya Engr Abba Kabir Yusuf murnar nasarar lashe zabe ba, ya kuma tabbatar da Kotun cewa duk kuri'un da aka kada an sanya masu hannu, ya kuma ce shi ne ya karbi sakamakon zaben Gwamnan a matakin Kasa, tare da tabbatar da cewa Abba Kabir Yusuf cikakken Dan Jam'iyyar NNPP ne ya kuma karanta Katin Jam'iyyarsa
Da yake amsa tambayoyi gaban Kotun Dr Aminu Idiris Harbau ya tabbatar wa da Kotun cewa yana da masaniyar an gudanar da zabe a ranar 18 ga watan maris, sai dai ya bayyana cewa ba shi da Kwarewa a fannin kimiya da lissafi biyo bayan tambayar da Lauyan Jam'iyyar NNPP yay masa.
Daga nan sai Kotun Mai Alkalai uku Karkashin Jagorancin Oluyemi Akintan Osadebay ta dage cigaba da zaman zuwa 20 ga watan Yulin 2023 domin fara sauraron shaidun kariya daga Hukumar zabe (INEC) za ta gabatar.