Da alama jawabin shugaban kasa bai wadatar ya hana kungiyar kwadago tsunduma yajin aiki ba yayin da suka dage cewa za a fara yajin aikin daga gobe Laraba.
Kungiyoyin da suka hada da kungiyar kwadago ta NLC da TUC, sun bayyana hakan ne bayan wata ganawa da suka yi da wakilan gwamnati a fadar shugaban kasa a daren jiya.
Shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero, ya ce shirin ma’aikata na gudanar da zanga-zangar lumana tun daga ranar Laraba bai canza ba.
Ya nuna shakku dangane da yadda shugaban kasa Bola Tinubu zai iya shawo kan hauhawar farashin kayayyaki da farashin man fetur yadda ya kamata saboda Rikiciwar farashin canjin kudaden waje.
Sai dai an dage taron zuwa karfe 12 na rana a yau Talata 1 ga watan Agusta 2023.