Sabon gwamnan jihar Kano,Ya bada umarnin cewar daga ranar 1 ga watan gobe na Yuni,Ya zama wajibi dukkanin wasu motoci dake bin titinan jihar kano da kuma Shagunan siyar da kayayyaki, su kasance suna da kwandon zuba shara a wurarensu, domin tabbatar da tsaftace jihar kano.
Domin tabbatar da wannan kudiri, Gwamnan na Kano, Abba Kabir Yusuf, Ya yi alkawarin kafa kwamitin kartakwana kan kwashe shara da yashe magudanan ruwa da kuma tsaftace hanyoyi, mai taken, Operation Nazafa.
Ya ce nan da ‘yan kwanaki masu zuwa zai kaddamar da gangamin tare da kungiyoyin temakon kai da kai domin tabbatar da aikin na kwamitin kartakwana.
Bugu da kari yayi alkawarin kwashe dukkanin wata tarin shara da aka zubar tare da yashe magudanan ruwa nan da ‘yan makwanni masu zuwa, da kuma tabbatar da samar da dorarren tsarin kula das u da kuma tsaftace su.