On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Wajibi Ne Ma'aikatanmu Su Bayyana Kadarorinsu - Shugaban EFCC

Shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC Ola Olukayode ya umarci daukacin ma’aikatan hukumar su gagauta ayyana kadarorin da suka mallaka bisa tanain tsarin aiki.

Mai Magana da yawun hukumar ta EFCC Dele Oyewale shine ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa, yace shugaban ya bada umarnin a wata ganawa da ma’aikata dake shalkwatar EFCC a Abuja.

Oyewale ya ambato Olukoyede yana cewa dole ne a rayu ta hanyar kafa tsari tare da kyawawan misalai.

A matsayin hukumar  dake  yaki da cin hanci da rashawa, dole ne hannayen ma’aikata su kasance da tsabta don haka wajibi ne kowa ya  bayyana kadarorin da ya mallaka.

Da yake kira ga ma’aikatan hukumar da su mai da hankali sosai kan yadda ake yaki da laifukan tattalin arziki da hada-hadar kudi, Olukoyede ya ce kamata ya yi a mayar da irin wannan kokari wajen bunkasa tattalin arzikin al’umma, da samar da yanayi mai kyau na bunkasa zuba jari da kuma karfafa tushen tattalin arzikin kasa.