On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Victor Oshimhen Ba Na Sayarwa Ba Ne

victor

Dan wasa Victor Osimhen ba na siyarwa bane kamar yadda Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Napoli, Aurelio de Laurentiis, ya sake nanata hakan a ranar Alhamis bayan matsin lamba da wasu manyan kungiyoyi suka yi na sayen dan wasan na Super Eagles.

Idan  ba’a manta  ba  an rika  danganta  dan wasa  Osimhen da komawa kungiyar Al Hila ta Saudiya  bayan da Man United da Chelsea da  Bayern Munich da PSG suka fara nuna sha'awar sayan  shi.

Sai dai a halin yanzu  shugaban kungiyar  ya  ce  babu wannan magana.