Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta kasa JAMB reshen jihar Kano, tayi kira ga ‘Daliban da sukayi rijista amma ba su rubuta jarabawar UTME ta bana ba, dasu kai korafinsu ga ofishin Hukumar dake a yankin Farawa a karamar Hukumar kombotso.
Hakan dai na zuwa ne bayan samun korafe-korafe da dama daga ‘Daliban da sukayi Rajista domin Rubuta jarabaawar, wadanda basu samu Damar Rubutawa ba kamar yadda aka tsara a sakamakon kura-kurai da suka hadar da matsalolin internet da matsalar Dangwalen yatsa da kuma na Na’urar tantancewa a wasu cibiyoyin Rubuta jarabawabar.
Wani babban jami’in hukumar da ya Bukaci a sakaya sunansa ya yiwa wakiliyarmu Joy Godson karin haske , inda yace Hukumar ba zata lamunci kowanne irin korafi daga ‘Daliban da suka ki zaunawa jarabawar a lokacin daya kamata su Rubuta ko kuma wadanda suka isa cibiyoyin jarabawar a makare.
Sai dai ya yi fatan cewa dai Hukumar JAMB zata yi nazari kan ‘Daliban da abun ya shafa domin yin abun da ya da ce.