Yayin da ake ci gaba da gwabza yaki a gabashin Ukraine, A yanzu haka kasar ta samu gagarumin ci gaba a jiya, bayan da kungiyar Tarayyar Turai ta baiyana cewa a halin yanzu Kasar zata iya shiga cikin kungiyar, lamarin da ke nuni da wani gagarumin sauyi na siyasa da zai biyo bayan mamayar da kasar Rasha ta yiwa Ukrain.
A wani taron kolin da za a yi a mako mai zuwa, ana sa ran shugabannin kungiyar ta EU za su amince da shawarwarin da hukumar zartaswar kungiyar ta bayar ga Ukraine da makwabciyarta Moldova.
Shugaban kasar Ukraine VolodymyrZelenskiy Ya wallafa wani sako a shafin Twitter wanda ya baiyana cewa bajintar da 'yan kasar suka nuna ya zama wani abun tarihi da Kungiyar Taraiyyar Turai zata kara samar da wasu damammaki a kasar.