Mataimakin shugaban jamiyyar Labour Lamidi Apapa ya tsaya akan bakan shi kan cewa shine mukaddashin shugaban jamiyyar ta kasa, kuma yana amfana da goyon bayan dan takarar shugaban kasar jamiyyar Peter Obi wadanda aka fi sani da Obidients.
Idan za’a iya tunawa dai a makon daya gabata ne, Apapa ya ayyana kansa a matsayin shigaban jamiyyar Labour biyo bayan wani sabon rikici daya kunno kai a jamiyyar.
Yayin da yake ganawa da gidan talabijin na Channels a daren jiya, Apapa yace shine mukaddashin shugaban jamiyyar ta kasa sannan kuma ya musanta zarge zargen da ake yin a cewa shine ke daukar nauyin yan hamayya don su ruguza jamiyyar.
Sai dai kuma shuwagabannin jamiyyar Labour a jihohi 36 na kasar nan sun jaddada cewa har yanzu Julius Abure shine shugaban jamiyyar.
Shuwagabannin jamiyyar a jihohi sun bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da manema labarai a Abuja a karshen makon daya gabata.
Da yake karanto takardar bayan taro bayan ganawa da shuwagabannin jamiyyar a sakateriar jamiyyar, shugaban jamiyyar reshen jihar Edo Ogbaloi Kelly ya sake tabbatar da cewa kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun tabbatar da Abure a matsayin shugaban jamiyyar na kasa.