Ana sa ran tsohon shugaban kasar Sri Lanka Gotabaya Rajapaksa zai dawo kasar daga Singapore.
Kakakin majalisar ministocin kasar Bandula Gunawardena ya fadawa manema labarai a ranar Talata cewa Mista Rajapaksa bai boye kansa a wani wuri ba, kuma zai iya dawowa gida kowane lokaci daga yanzu.
Tsohon shugaban kasar ya tsere daga kasar Sri Lanka bayan tarzomar da ta barke a kasar saboda tabarbarewar tattalin arziki.Da yawa daga cikin masu zanga-zangar sun ce ya karkatar da akalar kudaden kasar, lamarin da ya janyo tashin farashin kayayyakin masarufi.
Mista Rajapaksa ya bar Sri Lanka a ranar 13 ga Yuli zuwa Maldives, kafin ya wuce zuwa Singapore a ranar 14 ga Yuli.