On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Tsohon Shugaban Jam'iyyar APC Injiniya Karaye Ya Kama AIki Amtsayin Sabon Shugaban ADP A Kano

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na Kano, Engr. Bashir Yahaya Karaye ya zama shugaban riko na jam’iyyar ADP a Kano inda ya kama aiki a ranar alhamis.

Jam'iyyar ADP tana cikin kananan jam'iyyun siyasa dake tasowa kuma ake jin amon su a siyasar Kano gabanin manyan zabukan 2023 bayan NNPP da PRP dake gogayya da PDP da kuma APC mai mulki.

Karaye ya shiga offishinsa a yau amatsayin sabon shugaban jam'iyyar a yau Alhamis

Tunda farko bayan nadin da aka yi ma sa, Bashir Karaye ya fadawa manema labarai a Kano tare da jiga-jigan jam’iyyar ADP, cewa  shalkwatar jam’iyyar ta kasa ta tabbatar da nadin  a ranar 16 ga watan Satumban  kuma an rantsar da shi a ranar.

Wata sanarwa da kakakin majalisar jam’iyyar ADP ta yakin neman zaben gwamnan jihar Kano, Abbas Yushau Yusuf ya fitar, ta ce mukaddashin shugaban jam’iyyar na jiha zai hada kai da dan takarar gwamna na jam’iyyar a Kano Sha’aban Ibrahim Sharada domin dora tsarin dimokuradiyya na gaskiya kuma mai inganci.