Tsohon Sakataren Gwmanatin Taraiyya, Engr. Babachir David Lawal, Yayi fatali da matakin aiyana Kashim Shettima a matsayin Dan takarar Mataimakin shugaban kasa, na jam’iyyar APC mai mulkin kasa zabe mai zuwa.
A ranar Lahadin data gabata ce, Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu ya aiyana kashim Shettima a matsayin wanda zai yi masa takarar mataimaiki, al’amarin da ya dumama musayar ra’ayi a tsakanin al’umma.
Kazalika shima Babachir David Lawal,m wanda ya kasance mai goyon bayan Tinubu, Yayi tir da matakin da Dan takarar shugaban kasar ya dauka.
Wata sanarwa da ya fitar a daren jiya, Tsohon sakataren gwamnatin taraiyyar, Ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi amfani da karfin ikonsa na kwamandan Askarawan Najeriya da kuma kasancewarsa jagoran jam’iyyar APC na kasa, wajen soke nadin da aka yi.