Tsohon Ministan Shari’a na kasa, Abubakar Malami ya musanta rahotannin dake cewar ya cika wandonsa da iska, saboda zarginsa da aikata lefukan cin hanci.
Biyo bayan dakatarwar da aka yiwa shugaban hukumar EFCC, Abdulrashid Bawa, An samu wasu rahotanni dake baiyaana cewar, Tsohon ministan shari’ar ya fice daga kasar nan, domin kaucewa yunkurin kama shi tare da yi masa bincike.
Wata majiya daga hukumar EFCC, ta fadawa jaridar Daily trust cewar, Hukumar EFCC na bukatar samun bayanai daga wajen Abubakar Malami kan zarginsa da hannu, wajen siyar da wata gangar danyen milyan 48 ta barauniyar hanya, akan kudi Dala Bilyan 2 da milyan 400 a shekarar 2015.
Majiyar ta ce hukumar ta gaiyaci tsohon ministar shari’ar na kasa, to sai yaki amsa gaiyatar da hukumar ta yi masa.
To sai Malamin ya musanta rahotannin dake cewar baya Najeriya, Inda ya baiyana cewar yau juma’a zai halarci wani daurin aure a masallacin Marigayi Sheik Isyaka Rabiu dake nan kano da karfe 2 na rana.