Tsohon ministan yankin Neja Delta, GodsDay Orubeebe Ya fice daga jam’iyyare PDP, Sakamakon Abunda ya baiyana na rashin aiwatar da tsarin Dimukuradiyya.
Cikin wata wasika daya aikewa shugaban jam’iyyar na kasa ,Iyorchia Ayu, mai dauke da kwanan watan yau Litinin 20 ga watan da muke ciki, cikin wasikar Orubebe ya shaida cewa ficewa daga jam’iyyar batare da bata Lokaci ba kuma ya sanar da shugaban mazabarsa a karamar Hukumar Buturu a jihar Delta
Orubebe ya kuma nuna damuwa kan Gazawar jam’iyyar wajen kin amfani da tsarin karba-karba wajen bada tikitin takarar shugaban kasa, yana mai cewa bashi da niyyar sake karbar wani mukami daga gwamnatin shugaban kasa buhari a shekarar 2023
Tsohon ministan ya kuma bayyana cewa halin da jam’iyyar PDP ke ciki a yanzu bai nuna cewa jam’iyyar a shirye take ta kwato mulki a zaben 2023 ba.