Tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Farfesa Onje Wado da aka yi garkuwa da shi a yanzu ya kubuta.
Wado, wanda aka yi garkuwa da shi daga gidansa da ke Rinza a daren ranar Alhamis, ya kubuta ne bayan ya biya Naira miliyan 4 a matsayin kudin fansa.
Wata majiya daga danginsa ta ce masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan 70, amma dangin sun tattauna kuma a karshe suka biya Naira miliyan 4 kafin a sako shi.
Shima wani tsohon kwamishinan yada labarai a jihar Dogo Shamma ya tabbatar da sakin Farfesa a daren jiya.