Da alama rikicin da ya dabaibaye zaben fidda gwani na babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Kano na iya zuwa karshe yayin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce ta sanya ido kan zaben fidda gwani da bangaren Shehu Wada Sagagi ke jagoranta.
Kwamishinan zabe na hukumar INEC a jihar Kano, Riskuwa Arabu Shehu, ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa, a lokacin zaben fidda gwani, shari'a ta amince da tsagin da Sagagi ke jagoranta.
Riskuwa ya bayyana cewa, wasikar da shugaban jam’iyyar PDP ya aike wa hukumar ta bayyana sunayen wadanda suka sanya idanu a zaben daga shalkwatar jam’iyyar PDP ne kawai.
Sai dai ya jaddada cewa doka ba ta tilasta INEC ta amince da duk wani suna da jam’iyya ta gabatar daga zaben da ba ta sanya ido akai ba.