On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Tsaffin Takardun Naira Sun Sauka Daga Tsarin Halarcin Hada-Hadar Kudi A Najeriya - CBN

Babban Bankin kasa CBN yace daga ranar 10 ga watan Fabarairu da muke ciki na 2023 tsaffin Takardun Naira 200 da 500 da kuma dubu 1 sun daina aiki amatsayin halartattun Kudi a Najeriya.

Tun da farko dai CBN ya sanya ranar 31 ga watan Janairu a matsayin wa’adin da za ‘a daina  amfani da tsofaffin takardun kudi sai dai ya tsawaita sakamakon matsin lamba daga ‘yan Najeriya.
 

Duk da haka kafin wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu da aka kara, jihohin Kogi da  Kaduna da Zamfara sun garzaya kotun koli, suna neman a hana CBN daina amfanida tsaffin takardun kudin.
 

Kotun ta amince da rokon  ta kuma dage sauraron karar zuwa gobe Laraba  15 ga watan Fabrairu.
Da yake tsokaci kan al’amarin  a wata zantawa da yayi da ‘yan jarida, Konturola a bankin CBN a Bauchi, Haladu Idris Andaza, yace tsofaffin takardun ba sa kan doka.