Jami’an Yansandan da suka yi ritaya, wanda ke karkashin tsarin temake-keniyar biyan fanso, sunyi wata zanga-zangar lumana a nan kano, bisa abunda suka baiyana na tsantsar rashin adalci da ya daibaibaye tsarin biyan fanshon.
Jim kadan bayan wani taron koli na gaggawa da suka gudanar a filin wasa na Sani Abacha dake nan Kano, Tsaffin Jami’an Yansandan sun gabatar da zanga-zangar lumana, inda suka rika kokawa kan yadda hukumar kula da biyan fansho ke tafiyar da tsarin temakekeniyar biyan fansho na kasa.
Jagoran masu zanga-zangar, wanda kuma shine shugaban kungiyar tsaffin jami’an yansanda a nan Kano, Yunusa Yahaya Madaki, Yayi zargin cewa, hakkokinsu na fansho da kuma gratuity ana karkarkatar dasu ne kawai zuwa ga wata biyan bukata ta kashin kai.