Tashin gwauron zabi da farashin takin zamani yayi a kasar nan, Ya tilastawa manoma a nan jihar Kano yin amfani da Gishiri da kuma kanwa wajen yin nomansu.
Wasu manoman sun baiyana cewa, a baya suna amfani da gishiri da kanwar ne kawai domin kara inganta takin, to amma a bana abun yasha banban, inda suke amfani dasu kadai wajen yin nomansu.
To sai dai kuma masana sunyi gargadin cewa yin amfani da wannan hanya zai illa ga kasar da ake noma a kanta, inda suka bada shawarar yin amfani da takin gargajiya.
A yanzu haka dai farashin takin zamanin ya haura dubu 25 inda a wasu ke yake kaiwa har kusan dubu 30.
Tsadar takin na zuwa ne a yayin da gwamnati ke ikirarin bijiro da shirye-shiryen bunkasa aikin gona da kuma tallafawa manoma a Najeriya.