On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Tsadar Kayayyaki Na Yiwa Kamfanoni Barazanar Rufewa A Najeriya

‘Yan kasuwar man fetur na kokawa  kan matsalar canjin kudin kasashen waje a Najeriya da kuma aiwatar da karin haraji na kashi 7.5 akan  man dizal a kwanakin baya, wanda ya sa farashinsa farashin ya tashi zuwa Naira 900 zuwa 950 kowacce litta.

Hakan acewar masana'antun gida, na iya haifar da rufe wasu masana'antu da asarar ayyukan yi.

‘Yan kasuwar da ke karkashin kungiyar masu samar da mai da iskar gas ta Najeriya sun tabbatar da hakan jiya a wani taron manema labarai a Abuja.

Shugaban su na kasa, Benneth Korie, ya ce farashin man dizal ya kai kusan Naira 650 kowacce litta kafin a bullo da harajin kashi 7.5 cikin 100 tare da rashin samun dalar Amurka.