Matukar ba wani sauyi aka samu ba, Rahotanni na baiyana cewar shugaban kasa, Bola Tinubu zai aike da sunayen mutanen da yake son nadawa a matsayin ministoci a gwamnatinsa, da zarar an kammala hutun babbar sallah, ga majalisar dokoki ta kasa domin tantancewa.
A yaune ake saran shugaban kasar zai dawo gida Najeriya da birnin Landan, inda zai wuce zuwa birnin Ikko domin yin idin babbar sallah.
Shugaban kasar ya zarce zuwa Burtaniya daga kasar Faransa inda ya halarci taron tafiyar da harkokin kudi na duniya, wanda shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya karbi bakuncin taron.
Jaridar Punch ta Ambato wata majiya na baiyana cewar, kusan an kammala rubuta sunayen ministocin da Tinubun zai nada a gwamnatinsa, inda za’a tura su majalisa domin tantancewa bayan hutun babbar sallah.