A yaune shugaban kasa Bola Tinubu zai ta shi daga Abuja zuwa masarautar kasar Netherland domin yin wata ziyarar aiki.
Wata sanarwa da kakakinsa Ajuri Ngelale ya fitar, ta baiyana cewar shugaban kasar zai kuma halarci taron majalisar bunkasa tattalin arziki ta duniya, wanda za’a yi ranar 28 zuwa 29 ga watan da muke ciki a kasar Saudiyya.
Sanarwar ta kara da cewar, Gaiyattar da Firiyiministan kasar Netherland Mark Rutte ya yiwa shugaban kasa Bola Tinubu, za taba muhimman batutuwan samar da cigaba, sannan kuma zai gana da sarki Willem Aleander da sarauniya Maxima ta masarautar.
Kazalika shugaban kasar zai halarci taron ‘yan Najeriya dake gudanar da harkokin kasuwanci da zuba jari a kasar ta Netherland , wanda zai tattauna kan hanyoyin da kasashen biyu zasu ci gajiyar juna ta bangaren yin kawance, musamman aikin gona da kuma sarrafa albarkatun ruwa da ake da su.